Sankarau ce ta kashe mutane a Kano ba sabuwar cuta ba – Kwamishina Getso

0

A ranar Laraba ne kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kano Kabiru Getso ya bayyana cewa sun gano cutar da ta kashe mutane takwas a kauyen Dungurawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

Idan ba a manta ba a ranar 26 ga watan Maris ne wata cuta ta bullo a kauyen inda mutane takwas suka rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar wanda hakan ya sa gwamnati ta gaggauta aikawa da ma’aikatar kiwon lafiya domin binciko irin cutar.

Ya ce sakamakon ma’aikatan kiwon lafiya da ak tura kauyen ya tabbatar musu cewa cutar sankarau ce ta yi ajalin wadannan mutane ba cutar da ba a san ko wace iri bace.

” Binciken da suka gudanar ya nuna cewa tun a ranar 15 ga watan Maris ne cutar ta fara bullowa sannan mutanen sun mutu ne sanadiyyar kin zuwa asibiti a lokacin da suka kamu da cutar.”

Getso ya ce domin dakile yaduwar cutar gwamnati za ta aika da ma’aikatan kiwon lafiya domin gano wasu da suka kamu da cutar da kuma wayar wa mutane kai game da hanyoyin da za su bi don gujewa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author