Sanata Bukar Abba, na jihar Yobe, ya bayyana cewa a zaman yanzu ana ci gaba da tattauna ganin Boko Haram sun sako Leah Sharibu kwanan nan ba da dadewa ba.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin da ya sa baki a zauren Majalisar Dattawa bayan Sanata Emmanuel Bwacha na jihar Taraba ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimin kokarin da suke wajen ganin an sako yarinya daya da ta rage daga cikin daliban Dapchi da Boko Haram suka sace a ranar 19 Ga Afrilu.
Sharibu dai na cikin daliban Dapchi 110,sai dai kuma duk an saki sauran, sai ita kadai ta rage.
Rahoton da wata yarinya ta furta bayan an sako su, ta ce an ki sakin Sharibu ne bayan ta ce ita ba za ta sanya hijabi ba, kuma aka yi mata tayin shiga musulunci, ta ce a’a.