Jami’an ‘yan sandan jihar Edo, sun gurfanar da wani dattijo mai shekaru 70 tare da dan sa a kotu, a bisa zargin su da yi wa yarinya mai shekaru 9 fyade.
Dattijon mai suna Francis Ezomo, da ‘ya’yan na sa Nosa da Fesus, ana tuhumar su ne da laifin hada kai a tsakanin su, su ka yi wa yarinyar fyade.
Yarinyar dai ‘yar uwar matar Ezomo ce, wadda ke zaune a hannun ta.
Yarinyar ta rika yin wadansu dabi’u a makaranta, wanda hakan ya sa malaman ta suka farga da cewa fyade ne aka yi mata.
Wannan magana ta firgita gwamnatin jihar, inda har Gwamna Godwin Obaseki ya bada umarnin a gaggauta cafke wadanda suka yi mata fyaden.
A cikin kotun, yarinyar kankanuwa ta barke da kuka, yayin da ta yi arba da mutumin da ya yi mata fyaden ga shi tsaye a gaban ta tare da sauran ‘ya’yan na sa biyu da aka kamo su tare.
A yanzu dai yarinyar na karkashin kulawar Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Edo.
Ita kuma babbar sakatariyar ma’aikatar mai suna Julie Olatunji, ta bayyana cewa masu fyaden sun ji wa yarinyar rauni. Amma yanzu ta na karbar kulawa a asibiti.
Su duka ukun dai sun ce atafau ba su taba yarinyar ba ma.
Alkali ya bada belin dattaijon mai shekara 70, amma ya hana belin ‘ya’yan na sa guda biyu.
Discussion about this post