Rundunar ‘Yan sanda ta ce Buhari bai rubuta wa Sufeto Janar takardar korafi ba

0

Rundunar ’yan sandan ta kasa ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne da ake yayada cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Sufeto Janar Ibrahim Idris takardar gargadi ko karafi ba, dangane da korafin da shugaban ya ce cewa Sufeto Janar din ya koma jihar Benuwai har bayan da aka shawo kan rikicin makiyaya da manoma a jihar.

Daga nan sai rundunar ta kalubalanci kowane ya gabatar da takardar da aka ce an aika wa Sufeto Janar, to ya fito da ita ya fallasa.

Wata sanarwa da aka ce daga fadar Shugaban Kasa take, an ce ta umarci Ibrahim Idris ya gaggauta komawa Benuwai.

Yayin da manema labarai ke ta zaman jiran karin haske, bincike ya nuna cewa dai Buhari bai rubuta masa wata wasika ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Jimoh Moshood ya bayyana wa THISDAY cewa ba a aika wa Sufeto Janar wasikar komai ba.

Ita ma fadar shugaban kasa ba ta maida wa PREMIUM TIMES amsar da ta nema ji dangane da tabbacin aika wa da takardar koke da gargadin ga Sufeto Janar din ba.

Share.

game da Author