Rundunar yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa ba ta rike da wani katin shaidar shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar.
Kakakin Rundunar ya ce, Zakariya Idris wanda hoton sa ne a kan katin, shi ne shugaban kungiyar na Miyetti Allah na jihar, ya je ofishin DPO na karamar hukumar Bassa, ya kai rahoton cewa wasu mahara dauke da makamai sun kai hari a gidan sa inda suka tafi masa da wasu muhimman abubuwan sa da ya hada da katin shaidar sa da ke dauke da hoton sa.
An samu rahoton barkewar rikici tsakanin kabilar Irigwe da Fulani mazauna karamar hukumar Bassa a cikin jihar Filato, inda har aka kashe fararen hula da jami’an tsaro.
Kakakin jami’an tsaron Tyopev Terna, ya ce amma dai su ba su tsinci katin sa a ko’ina ba. Kuma idan ma wani ya tsinta, to har yanzu bai kai shi ofishin ’yan sanda ba.
Wannan bayani ya fito ne jim kadan bayan jaridar Punch ta buga labarin cewa an tsinci katin shaidar shugaban kungiyar Miyetti Allah ta jihar Filato da wayar selular sa a inda aka yi gumurzu tsakanin kabilar Irigwe da Fulani.
Dama kuma Kwamishinan Yan sandan jihar Undie Adie ne da kan sa ya fara musanta wannan zargin a wata hira da ya yi da PREMIUM TIMES jiya Lahadi da dare.