APC ta dauko hanyar tarwatsewa – Nyako

0

Tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya gargadi jamiyar APC da ta maida hankali wajen like ramukar dake yoyo a dakinta idan ko ba haka ba to dakin zai rushe warwas kowa ya kama gaban sa.

Nyako ya ce kara wa shugabannin jam’iyyar wa’adin da akayi kuskure ne kuma hakan zai iya zama kamar daba wa ciki wuka ne.

Nyako ya bayyana haka ne da yake ganawa da wasu ‘ya’yan jam’iyyar a wajen ta’aziyyar tsohon gwamnan jihar, marigayi Sale Michika.

“ Jam’iyyar ta kauce daga ainihin manufofin da aka kafa ta a kai kuma Idan dai ba bin dokar jam’iyyar aka bi ba na tabbatar da an gudanar da sabon zabe domin nada sabbin shugabannin jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta zo da shi ba, tabbas ko za a ga ba daidai ba.

“Ina so in tabbatar muku cewa ko makaniken mota ne ya kai Jam’iyyar APC kotu cewa ta karya dokar jam’iyyar na kin gudanar da zabuka a mukamai na jam’iyyar, hakan zai iya sa komai ya damalmale domin da zarar kotu ta tabbatar da haka sai dai jam’iyyar ta koma ‘yar kallo lokacin zabe.”

Ya gargadi jam’iyyar da ta dauki darasi daga abinda ya faru da jam’iyyar PDP a 2015 domin gujewa afkawa irin wannan kugiya.

“ Kalaman wasu daga cikin shugabannin a kasar nan yadda kasan mashayin Ogogoro ne, domin abin sai ka kasa gane gaban sa ballan tana bayan sa.”

Share.

game da Author