Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mutanen da aka kashe a fadan makiyaya da manoma a Mambilla ta jihar Taraba kadai, sun fi wadanda aka kashe a rikicin Benuwai da Zamfara dukan su.
Buhari ya bayyana haka ne a jiya Litinin a garin Jalingo, yayin da ya ke ganawa da Fulani da kabilun yankin. Buhari ya ce ya na da hanyoyin da ya ke samun dukkan bayanan abubuwan da ke faruwa dangane da kashe-kashen da duk ke faruwa a fadin kasar nan.
Buhari ya ce ya je Taraba ne domin ya yi gaisuwa kuma ya jajanta kan wadanda aka rasa, ya ce zubar da jini abu ne mummuna. Ya kara da cewa samar da zaman lafiya da tsaro ba aikin gwamnati ba ce ita kadai, sai an samu hadin kan Jama’a.
Daga nan sai ya yi roko da cewa a rika tabbatarwa an yi adalci ga kowane bangare, ya na mai cewa a tabbatar da an zakulo wadanda suka yi kisa an hukunta su.
A nasa bayanin, gwamna Ishaku Darius ya gode wa Shugaba Buhari tare da tabbatar masa cewa gwamnatin sa za ta yi iyakar kokarin ta wajen ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma ce za a hada kan sarakunan gargajiyar yankin domin a samu nasarar aikin samar da makamashi na Mambilla ‘Hydroelectric Power.’