Kingibe ya sa mun loda wa farkar sa tulin daloli bayan wanda ya ke jida -Jami’in NIA

0

Jami’an Hukumar EFCC sun shafe kwanaki biyu su na yi wa Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babagana Kingibe tambayoyi.

PREMIUM TIMES ta gano cewa Kingibe ya sha ruwan tambayoyin a ranakun Laraba da Alhamis da suka gabata, dangane da zargin wata harkallar makudan daloli da ake zargin ya duma hannun sa a ciki.

Wani jami’in tsaro da ya nemi mu boye sunan sa, ya tabbatar da cewa an yi wa Kingibe tambayoyin ne a ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro.

Kingibe dai ya tsunduma kan sa a cikin badakalar a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi shugabancin kwamitin da zai yi nazarin ayyukan Hukumar Tsaro ta Sirri ta Kasa (NIA). An nada Kingibe shugabancin kwamitin ne a cikin watan Nuwambar 2017, kuma tuni kwamitin ya kammala binciken sa har ya damka wa Buhari rahoto.

Sai dai kuma ashe Ambasada Kingibe ya bar baya da kura, har ma da kaikayi, yayin da aka zarge shi da harkallar kudaden Hukumar NIA a lokacin da ya ke aikin da Buhari ya nada shi.

A kan wannan ne EFCC ta gayyace shi domin ya bayyana rawar da ya taka a wajen salwantar wasu makudan kudade.

Da farko dai, Dauda Mohammed wanda ya kasance Shugaban Riko na Hukumar NIA a lokacin da Kingibe ke binciken sa ne da kan sa ya zargi shi Kingibe da rika karbar kudade daga hukumar haka kawai.

Idan ba a manta ba, Dauda ya shaida wa hukumar Kwamitin Majalisar Dattawa da ke binciken zargin yadda aka nemi wata dala miliyan 44 daga aljihun NIA, amma ko sama ko kasa, cewa Kingibe ya rika takura masa ya rika ba shi duk abin da ya tambaya a ba shi.

To daga nan ne sai Majalisar Tarayya ta umarci EFCC ta bincika zargin da ake yi wa Kingibe da kwamitin sa.

Sai a ranar Larabar da ta gabata ne EFCC ta kira Kingibe inda ya bayyana a gaban matambaya, aka rika sheka masa ruwan zafin tambayoyi kan zargin da ake yi masa. Daga nan ake ce ya tafi gida, washe gari Alhamis ya koma.

An ce Kingibe ya yi kememe ya musanta zarge-zargen da Dauda Mohammed ya yi masa.

Yayin da ya koma ranar Alhamis, sai aka kira Dauda Mohammed, ga shi ga Kingibe, aka ce ya karanto dukkan zargin da ya ke wa Kingibe.

An ce daga nan ya rika lalo harkalla da kwatagwangwamar da Kingibe ya yi da kudaden NIA a lokacin da ya ke shugabancin kwamitin shugaban kasa. Sai dai kuma duk wanda aka karanto, sai ya ce bai san da su ba.

“Amma dai Kingibe ya amince da cewa ya na karbar naira miliyan daya da rabi a kowane sati a matsayin kudin kama daki a otal din da ya ke sauka, baya da abincin da hukumar NIA ke sai masa.” Haka majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar.

Sannan kuma Kingibe ya amsa zargin ya rika daukar motocin hukumar NIA tare da jami’in tsaro ya na zuwa Bauchi.

Abin sai da ya kai har da zargin bahallatsa kan Kingibe. Mohammed ya yi zargin cewa Kingibe ya sa sun bai wa wata farkar sa tsabar kudi na kasashen waje, a bisa umarni shi Kingibe din. Sai dai shi kuma wanda ake zargi ya ce bai san wannan batu ba.

Majiya ta ce irin wannan barankyankyama ta na da wuyar sha’ani domin ita dai NIA ba rasidai ko invoice ta ke ba yarwa ba, ballantana a yi saurin kama mutum dumu-dumu.

PREMIUM TIMES ta yuntubi kakakin EFCC Wilson Awujeran, ya ce ba shi da labarin ko an yi bincken.

Share.

game da Author