Ana zargin Gidan Marayun Kaduna na saida marayun da aka damka musu amana

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta damu kwarai da zargin da ake yi wa Gidan Marayun Kaduna cewa su na saida marayun da aka damka musu amana ga baki daga kasashen waje.

An dai yi zargin ne sakamakon wani hukuncin da Babbar Kotun Kaduna ta bayar cewa a damka wasu yara uku ga wani dan kasar Ghana da gwamnati ta yi zargin cewa sayen yaran ya yi da tsabar kudi har naira milyan 1.1.

Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Hafsat Baba ce tabayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da jaridar PREMIUM TIMES a ranar Asabar.

Ta ce gwamnatin jihar Kaduna na fargabar cewa ana neman a maida jihar wata cibiyar hada-hadar fataucin kananan yara.

A ta bakin ta, ta bayyana cewa kwanan nan kuma an ja hankalin ma’aikatar ta dangane da harkallar saida wani yaro a kan kudi naira milyan 2.5 da aka yi ga wani dan kasar waje. Ta ce yaron kuma daga Gidan Marayun Kaduna aka sayar da shi.

Hafsat a cikin haushi da takaici, ta bayyana wa PREMIUM TIMES yadda a cikin shekarar da ta gabata kiri-kiri yadda alkali ya kayar da jihar Kaduna a shari’ar wasu yara kanana, inda ya yanke hukuncin cewa a damka su wurin wannan dan kasar Ghana, wanda shi zargin sa aka yi ya sayi yaran ne a kan kudi naira milyan 1.1 daga wani asibiti a Zaria.

“Ya sayi yara biyu maza a kan naira dubu N350,000 kowanen su, sai kuma wata yarinya mace a kan naira dubu N400,000 ita kadai. Mun shaida wa jami’an ‘yan sanda, sun kama shi, sannan suka kwace yaran daga gare shi.

“Daga nan sai gwamnatin jihar Kaduna ta karbi amanar yaran, aka saka su a makaranta, amma sai wani dan kasar Ghana lauya da ke aikin lauya a nan jihar, ya maka mu kotu a madadin wancan dan kasar Ghana da ya sayi yaran.

“Mun rubuta wa Ma’aikatar Shari’a wasika inda suka karbe shari’ar, to amma wani alkalin kotun majistare ya bada umarnin a maida yaran ga dan kasar Ghana din. Mu kuma mu ka ki, sai muka daukaka kara zuwa babbar kotun jiha.

“Lauyan nan dan Ghana da ya tsaya wa wancan dan Ghana wanda ya sayi yaran, ya zo ya same ni, ya ce mu sasanta kafin a zauna kotu. Na ce masa a’a, ai shari’a ce tsakanin dan Ghana da gwamnatin jihar Kaduna.

“Da lauyan nan ya fusata, sai kawai ga shi ya zo min da dan sanda da sammace wai a kama ni tunda na ki bin umarnin kotu, wato na ki damka wa wanda ya ke karewa yaran.

“Ni kuma na shaida masa cewa ba shi da ikon shigowa cikin ofishin gwamnati ya tayar da hanyaniya.

“Daga nan sai na shaida masa cewa ya je Ma’aikatar Shari’a saboda su ne shari’ar ke hannun su a madadin gwamnatin jiha.

Yayin da ya nemi ya wuce-gona-da-iri, sai na kira Kwamishinan Shari’a, sai ya turo mashawarci kan shari’a wanda ya zo ya karbi takardar sammacen.

“Daga nan sai aka bada umarni daga kotu cewa kada a kara ganin sa a harabar ofishi na ya na yi min wata barazana.

“To na bar maka magana baya, da lauyan nan dan Ghana ya zo ofis ya same ni, sai na tambaye shi ko wani daga wata kasa ko a cikin kasar su zai iya zuwa Ghana ya sayi yaro ya zaro kudi ya biya? Lauyan nan ya ce min a’a. Daga nan sai na tambaye shi, ta ya zai zo Nijeriya ya yi abin da ba zai iya yi a Ghana ba?

“In gajarce maka labari, lokacin da aka maida shari’a babbar kotu a nan Kaduna, sai aka ce mu je da yaran su uku a kotu.

Yayin da mai shari’a ta gan su, abin mamaki da al’ajabi, sai mai shari’a Hannatu Balogun ta ce gwamnati ba ta da gaskiya, mu damka yaran ga wannan dan Ghana wanda ya yi ciniki, hada-hada da safarar yaran.

“Kiri-kiri matar nan ta ce mu gaggauta damka yaran nan a gaban ta ga mutumin nan dan Ghana. Mutumin nan fa da kan sa ya rubuta cewa sayen su ya yi.

“Amma mai shari’a ‘yar Najeriya, wadda ke wa gwamnati aiki, kuma ta na sane da cewa gwamnati ta haramta fataucin yara ana saida su, ta fito a bainar jama’a ta yanke wannan danyen hukunci.”

Da PREMIUM TIMES ta tambayi kwamishinar dalilin da ya sa mai shari’a Hannatu Balogun ta ba gwamnati rashin gaskiya, sai ta ce ai abu ne a duhu, ba ta sani ba.

“Ni dai ban san dalili ba, amma dai ta yanke hukuncin cewa mu damka yaran.

Wannan hukunci ya jefa mu cikin damuwa, saboda a lokacin mu na da wasu shari’un na fataucin yara har guda shida daban-daban a kotu. Kuma mu na gudun kada duk mu rasa yin nasara a sauran shari’un.” Inji Hafsat.

A karshe ta ce a yanzu ba ta san halin da yaran su ke ciki ba, tun bayan damka su ga wannan dan kasar Ghana da aka yi, kamar yadda mai shari’a Hafsatu Balogun ta bayar da umarni.

Ta dai ce ta sanar wa Hukumar Hana Fataucin Jama’a ta Kasa (NAPTIP) halin da ake ciki.

Ta ce a yanzu dai Majalisar Jihar Kaduna ta kafa dokar hana fataucin yara, wadda nan ba da dadewa ba Gwamna Nasir El-Rufai zai sa mata hannu.

Share.

game da Author