Hukuncin kisa ya dace da masu safarar muggan kwayoyi -Bala Lau

0

Shugaban Kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Bala Lau, ya bayyana ra’ayin cewa kamata yayi a rika yanke hukuncin kisa kan dillalan muggan kwayoyi, domin hakan ya kamace su ganin yadda suke hallaka musamman matasan kasar nan.

Lau yayi wannan kira ne ga gwamnati yayin da ya ke nuna cewa irin yadda ake safarar muggan kwayoyi cikin kasar nan, abin tashin hankali ne ainun.

Ya ce muggan kwayoyi su ne a sahun gaba wajen lalata rayuwar matasa da al’umma.

Malamin ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke tattaunawa da PREMIUM TIMES a Kaduna. Ya na mai cewa nauyi ne da ya rataya kan gwamnati ta kare al’ummar ta daga shan muggan kwayoyi.

Ya ce Kungiyar Izala tare da Kungiyar Kiristocin Najeriya na kokarin ganin ana ci gaba da wayar wa mutanen Najeriya kai game da illolin da ke tattara da amfani da muggan kwayoyi kamar yadda suka yi wa cutar Kanjamau, kuma aka sami saukin yaduwar ta a kasar nan.

Share.

game da Author