Mai ba gwamnan Kaduna shawara kan harkar siyasa da ayyukan gwamnati, Uba Sani ya ziyarci Kasuwar magani domin yin ziyara gani wa Ido irin hasarar da mazaunan yankin suka yi sanadiyyar rikici da ya barke a Kasuwar.
Uba da tawagar sa sun ziyarci Kasuwar ne ranar Alhamis din da ya gabata, inda suka gana da mazauna yankin sannan suka duba irin taimako da gudunmuwar da za su iya kaiwa mutanen yankin.
” Na yi wannan ziyara ne domin in duba ku sannan in taya gwamnati rokon ku da mu zauna lafiya a tsakanin juna. Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai za ta yi duk abinda za tayi domin ganin irin haka bai sake faruwa.
” A matsayi na na dan wannan yanki wato Kaduna ta Tsakiya, ya zama mini dole in zo in zauna da ku sannan in duba irin abin da zan yi muku na gudunmuwa musamman ga wadanda suka rasa dukiyoyin su.
” Ina rokon ku da mu taru mu zauna lafiya, sannan mu taya jihar mu da addua domin samun dawwamammiyar zaman lafiya a jihar mu ta Kaduna. Sannan kuma mu more romon demokradiyya da gwamnan mu Nasir El-Rufai yake ta kokarin kawo mana jiha.
Mazauna yankin sun jinjina wa Uba sannan sun yaba masa da irin kokarin da yake ta yi wa mutane musamman na yankin Kaduna ta tsakiya ba karamar Kajuru ba kawai.
Abdussalam Malam wani mazaunin kasuwar magani ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa mutanen kasuwar magani sun yabawa Uba Sani musamman a wannan lokaci da suke bukatan irin wannan ziyara.
” Mu babu abin da za mu ce wa Uba sai godiya da fatan Alkhairi, domin ya nuna mana shi namu ne. Ya biyo mu har garuruwan mu sannan ya taimaka mana. Ya bamu shawarwari kuma ya nuna mana cewa shi na mu ne. Muna godiya. Dama can ya dade yana taimaka wa mutanen yankin nan musamman matasa.” Inji Abdussalam
Zaman lafiya ya dawo garin Kasuwar magani sananan gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a yankin.