Buhari ya biya wa dan Ajimobi sadakin ‘yar Ganduje

0

Shugaba Muhammadu Buhari da sauran manyan ‘yan siyasa irin su Bola Tinubu, da na daga cikin daruruwan jama’ar da su ka halarci daurin auren dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi da ‘yar gwamnan Kano, Fatima Ganduje, a ranar Asabar.

Shugaba Buhari ne ya kasance waliyin ango, wanda a al’adance shi ne zai nemi a ba shi auren ‘ya daga iyayen amarya, shi kuma ya ba da dan sa.

Ya dai nemi a ba shi Fatima ne daga bakin Bola Tinubu, wanda shi ne ya kasance waliyin amarya.

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II shi ne madaurin aure, kuma ya daura auren bayan da waliyin amarya, Buhari ya biya sadakin naira dubu 50,000 daga aljihun sa.

Kimanin gwamnoni 20 ne suka halarci daurin auren.

Share.

game da Author