Jami’in harka da jama’a na rundunar ‘Operatin Cat Race’ a jihar Benuwai Texas Chukwu ya bayyana cewa dakarun soji dake aiki a yankunan jihar sun kama wasu makiyaya bakwai suna barnata wasu gonaki. Ya ce sun kama hudu a gonakin dake kauyen Gbajimba, Kaseyo, Awe sannan uku a gonakin kauyukan Buruku, Uba, Abeda, Ameh da wata Fadama a Kuturu.
” Idan ba a manta ba dakarun sojojin rundunar sun kama wasu makiyaya 10 na baranata wasu gonaki a kauyukan Tse-Tigir da Tse-Ndugh ranar Litinin din makon jiya. Tsakanin kwanaki hudu dakarun sojojin sun kama makiyaya da suka aikata irin wannan laifin 17 kenan.”
Ya ce sun kama makiyayan dauke da makamai da dama a hannun su.