Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Daivd Misal ya tabbatar da wa manema labarai cewa mutane biyar sun mutu sannan da dama sun sami raunuka a sabuwar rikici da ya barke a karamar hukumar Sardauna, jihar Taraba
Missal ya bayyana cewa rikici ne ya barke tsakanin Fulani Makiyaya da was manoma. Ganin dama zaman doya da amanja ake kafin ace wata-wata an kaure da rikici inda ya bazu har zuwa kauyukan Nyiwa da Yerimaru.
” Sanadiyyar wannan rikicin an kona gidaje da dama sannan an kashe shanu da dama a rikicin.”
Wani mazaunin kauyen Gembu mai suna Abubakar Ardo mazaunin kauyen Gembu da ya tsira da ransa ya ce maharan sun biyo dare ne sannan suka farma yan kauyukan Fulani 15, suka kona su kurmus,
Misal ya ce zaman lafiya ya dawo yankunan da akayi rikicin.