An gano cewa ashe adadin jami’an ‘yan sandan kasar nan 371,000 da ake cewa ana da su, to ko kusa ba su kai ba. Wani bincike da PREMIUM TIMES ta yi a ofishin Akanta Janar na Tarayya, ya tabbatar da cewa gaba daya ‘yan sandan Najeriya su 291,685 ne kacal.
Kididdiga ta tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda na karbar albashin naira biliyan 22.3.
Hakan na yin nuni da cewa akwai na bogi su dubu 80,115 da ake karbar albashin su da alawus-alawus wadanda kwata-kwata babu su babu kuma labarin su.
Bayanan sun nuna ana biyan wadannan sunayen bogi biliyoyin kudade a kowace shekara, a tsawon shekaru da dadewa, kuma shugabannin ‘yan sandan sun kasa ganowa.
Ministan Harkokin Kudade, Kemi Adeosun, ta bayyana wa Shugaba Muhammdu Buhari cewa, na’urar kididdgige ma’aikata ta kididdige yawan ma’aikatar shiyyoyi da da ma’aikatu da hukumomi har 511, inda aka samu ma’aikata a cikin su har 607,834.