Wasu mazauna garin Soluyi/Sosanya da ke cikin jihar Lagos, sun bayyana yadda wasu mayunwatan birai ke barkowa cikin garin su, su na hana su sakat, har sai da suka kai ga raba su da gidajen su, suka gudu.
Sun bayyana dalilin guduwar ta su ce, ganin yadda biran su ka fi karfin su, har ta kai su na cinye musu abinci da karfin tsiya.
Garin dai ya na cikin jihar Lagos ne, inda suka yi kira ga gwamnatin jiha ta ceci al’ummar garin daga kuntatawar da biran ke yi musu.
Sun ce har ta kai biran na kutsawa cikin dakunan kwanan su da kukan dafa abinci, kantuna da shaguna, su na karya tagogi su shiga su cinye abinci da sauran duk abin da za su iya ci.
Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Haya a garin, Adigun Olaleye, ya bayyana cewa yanayin ya fa yi munin da mazauna garin ba su iya korar biran. Kuma barnar da suke yi ta kai makura.
Ya ce biran su na shiga garin ne saboda kusancin sa da wani daji mai duhu da ke tsakanin garin da yankin Ifako.
Ya ce a kowane lokaci suka ga dama, biran kan shiga garin, har ma da sanyin safiya, kuma su kutsa cikin gidaje, ko da kuwa an kulle.
Ya ce sun rubuta wasika ga Ma’aikatar Ayyukan Gona ta jihar Lagos, amma har yau ba su yi komai a kai ba. “Cewa suka yi sai dai mu biya su, sannan su zo su raba mu da biran.” Inji shi.
Olaleye ya ce tun shekaru masu yawa biran ka rike shigowa jifa-jifa, amma a wannan shekarar abin ya fi ta’azzara, domin har tawaga-tawaga ko runduna-runduna su ke yi su afko cikin garin.
Wata ‘yar jarida da ke zaune garin, mai suna Fummilola Gboteku, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa duk yada ka kulle gidan ka, sai biran sun kutsa kai a ciki.
Mazaunan garin da dama da aka yi hira da su, sun bayyana cewa sun dana tarko domin su rika kama biran, amma a banza. Wasu kuma sun rika zuba musu guba a abinci domin idan sun ci su mutu, amma da ya ke shegen wayau gare su, idan sun sinsina abinci sun ji warin guba, to ba su ci.
Wasu kuma sun ce sun fara harbin biran da bingida suna kashe su, amma tilas su ka daina, saboda ba karamin ganganci da kasada ba ne a rika dirka bindiga ta na tashi a cikinn gari, kuma tsakiyar jama’a.
Sun yi kira da gwamnati ta kai musu daukin gaggawa.