Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa gungun wasu tsirarun mutane sun hada kai su na ta kulle-kullen bata masa suna, ya na mai cewa shi dai har yanzu akidar sa ta gina ingantacciyar dimokradiyya na nan ba ta raunana ba.
“An jawo hankali na cewa ganin ba na Najeriya a yanzu ina kasar Saliyo domin sa-ido kan zaben raba-gardama da za a gudanar a kasar, wasu na nan su na ta kokarin lallai sai sun tozarta ni ko su zubar min da mutunci.’’
Jonathan ya ce magautan na sa ya samu labarin akwai na sarari da kuma na boye.
Jonathan dai shi ne shugaban sa-ido kan zaben Saliyo.
Ba a dai san dalilin da ya sa Jonathan wannan jawabi a shafin sa na soshiyal midiya ba, amma dai an ce hakan na da nasaba ne da wani rahoto da aka ce wani na kusa da shi ya yi kokarin jirkita sakamakon zaben 2015 ta hanyar biyan wani kamfanin kasar waje dala miliyan biyu domin ya dabbala sakamakon zaben, Jaridar Guardian ta Ingila ce ta ruwaito labarin.
Nan a gida Najeriya kuma, Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo, sun taso shi gaba, inda Buhari ya rika yi masa gorin rashin tabuka komai ga daliban Chibok da aka sace cikin 2014.
Shi kuma Osinbajo, kwanan nan ya ce a lokacun Jonahan an kwashe naira biliyan 100 daga Babban Bankin Tarayya, CBN, kwanaki kadan kafin a yi zaben 2015.
“Lokacin da ina mulki, na ce ba na fatan saboda neman mulki na a zubar da jinin ‘yan Najeriya, domin jini na bai fi na su daraja ba. Kuma ko yanzu a kan wannan akida na ke.
“Don haka duk irin bata suna da cin fuska da za a ci gaba da yi mini, ba zai yi tasiri ba.”
Discussion about this post