Abin takaici ne musanya sunan Gowon da sunan Buhari a titin Jos – Dalung

0

A ci gaba da sarar juna da akeyi tsakanin gwamnatin Jihar Filato da Ministan wasanni Solomon Dalung, abin ya koma cin fuska da tonan silili a tsakanin jami’an gwamnatin biyu.

Dalung ya na kalubalantar gwamnatin Jihar da ta bada bayanai kan miliyoyin dalolin da ta karbo bashi domin gina kamfanin sarrafa dankalin turawa a Jihar.

Sannan kuma ya yi tir da canza sunan titin da ada sunan tsohon shugaban kasa ne Yakubu Gowon aka maida shi titin Muhammadu Buhari.

” Wannan abu bai yi mini dadi ba ko kadan. Yayi matukar tada min hankali sannan abin takaici ne a canza sunan Dan asalin jihar wato Yakubu Gowon, asaka sunan bare , wanda na dan Jihar bane, wato Buhari. Ko a aikin soja Gowon na gaba da Buhari amma akayi masa cin fuska a Jihar sa.” Inji Dalung.

Dalung ya koka kan rashin gaiyatar sa ziyarar Buhari Jihar Filato da yayi wanda shine makasudin wannan zuba da yake ta yi.

Ko da yake gwamnati bata biye masa ba wajen maida masa da martani da irin Kalaman da yayi, kwamishinan yada labarai Yakubu Datti ya bayyana cewa, lallai Ministan Dalung ya bace cikin rubibi domin kuwa har yanzu gwamnatin Jihar bata karbi wannan bashi ba da yake ce wai sun karba sun handame.

” Ya je ya yi bincike ya gani ko gwamnatin Jihar ta karbi wannan bashi ko a’a. ”

Share.

game da Author