Majalisar Tarayya ta janye dakatarwar da ta yi wa Abdulmumin Jibrin

0

A yau ne majalisar tarayya ta janye takunkumin dakatarwar da ta kakaba wa Hon. Abdulmunin Jibrin daga Jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan wata wasika ne da ya rubuta ya aika wa majalisar ya na ba ta hakuri.

Duk da dai ba a karanta wasikar a sarari ba, amma Kakakin Majalisa, Yakubu Dogar ya ce Jibrin ya rubuto ya na bada hakuri, kuma ya cika sharuddan da suka kamata a maida shi majalisa.

An dai dakatar da shi tun cikin 2017, ya cika kwanakin zaman majalisar har kwanaki 180 a matsayin dakatacce.

Share.

game da Author