BOKO HARAM: ‘Sai sojoji da dakarun CJTF sun yi lalata da mu su ke ba mu isasshen abinci’

0

Kimanin wasu mata 1300 da ke tsare a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar Barno, sun rubuta wa Shugaba Muhammdu Buhari budaddiyar wasika, inda suka zargi sojoji da jami’an CJTF da cewa sai sun biya kudi ko kuma sun amince an yi lalata da su, sannan su ke samun wadataccen abinci a sansanin.

Matan dai sun bayyana cewa ana tsare da mazajen su ne tun cikin 2015 a bisa zargin cewa su ‘yan kungiyar Boko Haram ne, amma kuma ba gaskiya ba ne, su ba ‘yan Boko Haram ba ne.

“Ba a yarda mu rika fita daga cikin sansanin ba, domin sojoji ne ke tsare da mu. Kuma ba a ba mu wadataccen abinci, sai su rika cewa sai mun biya kudi sannan za su kara mana abincin. Su kuma mata masu jini a jika sai sojoji da CJTF sun yi lalata da su, sannan za su samu abincin da za su ciyar da ‘ya’yan su.”

Haka suka rubuta a cikin budaddiyar wasikar da suka rubuta wa Shugaba Buhari, kuma PREMIUM TIMES ta samu kwafen wasikar.

Matan sun ce mazajen su da ‘ya’yan su da ake zargi ‘yan Boko Haram ne, su na tsare har yanzu a barikin sojoji na Giwa, da ke Maiduguri da kuma kurkukun Maiduguri.

Sai dai kuma sojojin Najeriya sun karyata wannan mummunan zargi da suka ce an yi musu. Sun kuma kara da cewa karya ce da kuma kokarin bata musu suna da sage musu guyawun da suke samun karfin aikin kakkabe Boko Haram.

Wadannan mata dai sun roki da a gaggauta sako mazajen da ‘ya’yan su da suka ce ana tsare da su ne a bisa zargi, amma ba su da alaka da Boko Haram.

Sun rubuta wa Shugaban Kasa wasikar ce a karkashin wata kungiya da suka kira “Knifa Movement.’

Dukkan wadannan mata dai su na tsare ne a sannanin gudun hijira na karamar Hukumar Bama. Sun ce tun da aka kama mazajen da yaran su ba a taba gurfanar da su a gaban shari’a ba.

Sun ce baya ga halin zaman kuncin rashin mazaje da ‘ya’yan su da aka tsare, ana ci gaba da killace su da su da ‘ya’yan su mata a sansanin gudun hijira, ana tilasta yin lalata da su kafin a ba su abinci.

Wadannan mata sun kuma bada mummunan labarin irin yadda Boko Haram suka rika kai masu hare-hare can baya, ana karkashe musu mutane ana kwashe dukiyoyin su tare da ji musu fyade.
Sun kuma bayyana yadda ake yawan yin mutuwar fuju’a ta daruruwan mutane a asibitin sansanin ‘yan gudun hijira.

“Ba mu yi wa kowa fyade”

Onyeama Nwachukwu shi ne kakakin rundunar Operation Lafiya Dole. Ya bayyana zargin da matan suka yi wa sojoji a matsayin karya da kuma makarkashiyar sare wa sojojin gwiwa daga kokarin da suke yi.

Dangane da tsarewar da su ka ce an yi wa ‘yan uwan su, Nwachukwu ya ce shi ma hakan ba zai taba zama gaskiya ba.

“Mu ba mu tsare dangin wasu mutane a wurin mu, wadanda muke tsare da su wadanda ake zargi da kai hare-haren kunar-bakin-wake ne da kuma masu kai hare-haren sari-ka-noke.”

“Kuma yadda mu ke yi, shi ne idan muka yi bincke mu ka gano wadanda ba su da hannu, to sakin su muke yi. Amma duk wanda muka tabbatar da hujjojin ya aikata ta’addanci, ko ya taimaka wa masu ta’addanci to, mu na guranar da shi ne.”

Dangane da rashin yi musu shari’a har tsawon lokaci kuma, sai Nwachukwu ya ce wannan kuma sai su kai kukan su ga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, domin ita ce doka ta ba ta damar yin haka.

Kanar Nwachukwu ya ce iyaye mata ko matan wadanda aka zaga ko ake bincike ba su iya kafa shaida ko yanke hujjar cewa mazajen su ko ‘ya’yan su ba ‘yan Boko Haram ba ne. Kotu ce kawai za ta iya tabbatar da haka.

“Ai mun sha kama masu kai wa Boko Haram makamai da sauran kayayyakin da su ke amfani da su. Za ka samu wasu ba su taba daukar makamai sun yi ta’addanci ba, amma kuma su na taimaka wa Boko Haram, ko ta aika musu bayanai na sirri ko aika musu da kayan masarufi da kayan bukatun rayuwar yau da kullum zuwa can can inda su ke a boye. To ka ga duk wadannan ba lallai ba ne iyayaen su ko matayensu su san da wannan.”

“Ya kamata jama’a kuma su sani cewa ba fa Operation Lafiya Dole ne suka haifar da wannan halin kuncin da ake ciki ba.” Inji Nwachukwu.

“Yayin da a gefe daya mu ma mu ke jajanta musu halin da suke ciki, a gefe daya kuma ina so a fahimta ba Operation Lafiya Dole ne suka haifar musu da kunci ba. Laifin Boko Haram ne da suka rika kashe jama’a, su na sace ‘ya’yan su, su na tura su su kona kauyuka da gidaje.

“Mu aikin mu tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya. Domin mu ma mun samu kanmu a cikin wannan halin kunci, idan aka dubi yadda mu ke nuna kishi da saida rayukan mu wajen kare jama’a. Kowa ya san mu ne a sahun gaba.”

“Don haka su daina kallon mu a matsayin abokan gaba, Boko Haram ne abokan gabar mu gaba daya, mu da su.”

Share.

game da Author