‘Yadda ake tilasta matan Najeriya lalata da baki a kasar Italiya’

0

Jakadar Birtaniya a Najeriya, Laure Beaufils, ta bayyana tsananin damuwar ta kan irin halin da ‘yan matan Najeriya da ake safara zuwa kasashen waje ke fuskanta.

A yayin da ta ke jawabi a Benin, babban birnin jihar Edo, ta ce kusan sau 4000 zuwa 6000, duk wadanda ake lalata da su, tilasta musu ake yi, ba da son ran su ba. Kuma a haka za su ci gaba da kasancewa har karshen rayuwar su.

PREMIUM TIMES ta bi kadin taron wanda aka gudanar a Benin kan Matsalar Safarar Mutane zuwa kasashen waje.

Mataimakiyar Jakadar, ta ce abin fa ya kai makura sosai, kuma ya yi kamarin da tilas sai an dauki kwakkwaran matakin hana wannan safarar mutanen musamman mata.

Ita ma jakadar Kunguyar Turai a Najeriya, Ketil Karlsen, ta ce akwai matukar bukatar a gaggauta shawo kan wannan mummunar harkar safarar jama’a zuwa kasashen Turai.

Ta yi kiran a samu hadin kai tsakanin Najeriya da Tarayyar Turai domin a samu nasarar magance wannan matsala.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewa ta ware Yuro miliyan 47 domin kasheawa wajen shawo kan safarar mutane zuwa kasashen Turai.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyan cewa matsalar safarar ‘yan Nijeriya zuwa kasashen Turai na hana majalisar dattawa barci da saleba.

Ya kuma karfafa cewa su na bakin kokarin wajen ganin an kawar da wannan babbar matsala mai zubar da mutuncin kasar nan a idon duniya.

Saraki ya kara da cewa Najeriya ita ce kasa ta 23 daga cikin jerin kasashe 167 da ke da yawan bari a duniya.

Ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya ne aka fi safara ana fita da su ta mashigar Agadez da ke Jamhuriyar Nijar. Sannan kuma Najeriya ce ta biyar a jerin kasar da aka fi safarar mutane daga can ana bi ta tekun Mediterranean ana shiga da su Turai.

“Akalla ‘yan Najeriya 10,000 sun rasa rayukan su a kan hanyar su ta zuwa Turai tsakanin watanni shida kacal.
Saraki ya kuma gode wa gwamnan jihar Edo, Godwin Obasaki da ya shirya gagarimin taron shawo kan matsalar.

Share.

game da Author