Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a cikin shekaru 16 da PDP ta yi mulkin Najeriya, ta barnata dala biliyan 500 na ribar kudaden man fetur da kasar nan ta samu.
Buhari ya yi wannan jawabi ne a taron jiga-jigan jam’iyyar APC da aka gudanar a dakin taro na Gidan Gwamnatin Tarayya da ke Fadar Aso Rock, Abuja.
Shugaban ya kara da cewa ya karbi mulki a daidai lokacin da kasar nan ke daf da durkushewa.
“Abu ne mai sauki a manta da harkallar kudaden tallafin mai, harkallar cinikin makamai, dimbin basussukan da aka ciwo ba a biya ‘yan kwangila ba da sauran matsalolin da suka haddasa, duk kuwa da cewa an samu sama da dala biliyan 500 daga ribar danyen mai da iskar gas a cikin shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki.”
Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi kokari sosai a hawan ta mulki cikin kusan shekaru ukun da ta yi. Sai ya yi kira ga shugabannin APC da su daina jin kunyar bayyana dimbin ci gaban da gwamnati ta samu daga 2015 zuwa yau.
Ya dai amince cewa har yanzu akwai kalubalen harkar tsaro a kasar nan, amma duk da haka ai ko irin kasashen da suka fi ko’ina tsaro a duniya, su ma su na fuskantar irin wadannan matsalolin.
“Amma na tabbatar da cewa matakan da mu ke dauka za su kawar da kalubalen maharan da ake fama da su a cikin karkara, rikicin makiyaya da manoma, rikicin kabilanci, garkuwa da jama’a da sauran matsaloli.”
Da ya juya kan rikicin cikin gida na jam’iyyar APC, ya ce ya na da yakinin cewa za a warware komai musamman ganin cewa ya nada dattijo kuma jigon jam’iyyar APC, sanata Bola tinubu domin ya sasanta dukkan bangarorin da ba su ga-maciji da juna.
Ya kuma ja kunne jam’iyya cewa tunda zaben 2019 ya gabato, to a gaggauta yin taron kananan hukumomi da na jihohi na jam’iyya domin a za bi sabbin shugabanni.
Discussion about this post