Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu a kudirin kafa sabuwar rundunar tsaro na ‘Peace Corps’ a kasa Najeriya.
Shugaba Buhari ya ce gwamnati ba za ta iya samar wa irin wannan sabon hukuma kudaden gudanar da aiyuka ba sannan kuma da yanayin tsaron kasa.
Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ne ya karanta wasikar a zauren majalisa.