Jami’ar asusun UNICEF Ada Ezeogu ta bayyana cewa sama da yara miliyan 1.5 ‘yan kasa da shekaru biyar a kudu maso yammacin Najeriya na fama da rama.
Ezeogu ta fadi haka ne a taron wayar da kan mutane mahimmancin ciyar da yara abinci da ke dauke da sinadarorin da za su taimaka wajen inganta girman yaro wanda aka yi a Ibadan jihar Ogun.
Ezeogu ta ce bincike ya nuna cewa kashi 80 bisa 100 na yaran dake fama da irin wannan matsalar na zama a kasashe 14 a duniya wanda Najeriya na daya daga cikin su sannan ita ce ta biyu a kasashen da suka fi fama da wannan matsalar.
” Najeriya na da yawan yaran da suka fi fadawa cikin wannan matsalar miliyan 17 wanda daga ciki yara 277,462 na zaune a jihar Ogun ne.