Masu garkuwa sun sace iyalen ma’aikacin VOA, sun harbe ma’aikacin FRSC a Kaduna

0

Wani ma’aikacin ‘Voice of America (VOA)’ Nasir Birnin-Yero ya kokawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace matar sa da dan sa daya a daren Talata a Kaduna.

Birnin-Yero ya bayyana wa gidan jaridar haka ne ranar Laraba inda ya kara da cewa masu garkuwan sun shiga gidan sa ne dake Birnin –Yero da misalin karfe 1:30 na dare.

” Ko da suka shigo gidan sai suka tada dana da matata suka tilasta su, su kai su inda nake. Ana cikin haka ne sai wani makwabcina Sabitu Abdulhamid wanda ke aiki da hukumar FRSC ya fito daga cikin gidan sa domin ya kawo mana dauki sai barayin suka harbe shi har lahira.

Birnin Yero ya ce masu garkuwan basu tuntube shi ba tukuna.

Share.

game da Author