Shugaba Muhammadu Buhari ya bayanna dalilan da ya sa ya ki sa wa dokar kafa Rundunar Zaman Lafiya wato ‘Peace Corp’, bayan da aka rigaya aka tura masa kudirin kafa dokar tun cikin 2017.
Dalilan na kunshe ne a cikin wasikar da Buhari ya tura wa Majalisar Tarayya, kuma kakakin ta Yakubu Dogara ya karanta a sarari a zauren majalisa.
A cikin wasikar, Buhari ya bayar da dalilai na tsaro dangane da yanayin kaki ko kayan sarki da aka amince a dinka musu.
Akwai kuma dalili na biyu cewa duk wani aikin tsaro da ake so su yi, to akwai bangaren jami’an tsaron da ke gudanar da aikin.
Dalili na uku kuma shi ne matsalar makudan kudaden da za rika kashewa da kuma wannan za a kashe a wajen kafa su.
Ya kara da cewa tafiyar da harkokin kashe kudade na hukumar tsaro da za kafa sabuwa ful, ba karamin abu ba ne, musamman ma ganin cewa ana cikin yanayi na matsalar samun wadatattun kudaden shiga kasar nan ga gwamnatin tarayya.
RA’AYOYIN MAMBOBIN MAJALISAR TARAYYA
Dan Majalisar Tarayya daga jihar Delta, Ossai Nicholas, ya bayyyana cewa abin burgewa ne kwarai irin yadda Shugaba Buhari ya bayyana dalilan kin amincewa da kafa dakarun.
Nicholas ya ce dama ita doka aikin kafa ta ba a kan majalisar tarayya ya fara kuma ya kare kacokan a kan ta ba.
Ya ce amma duk da haka majalisa za ta zauna ta duba dalilan da shugaban kasa ya bayar ko abin dogara ne ko kuma a’a.
KAI RUWA RANA
Kusan kamar shekara daya da ta gabata ne hukumomin tsaro na sojojin Nijeriya tare da ‘yan sanda da kuma SSS suka yi yi wa hedikwatar Dakarun Zaman Lafiya dirar mikiya, suka cumuimuyi shugaban rundunar, wanda kuma shi ne ya kirkiro ta, watau Dickon Akoh, da sauran shugabannin da su ka taras a hedikwatar.
Tun daga lokacin ne ofishin ya ke a kulle. Daga nan kuma sai a cikin watan Maris, 2017, huumar ‘yan sandan kasar nan ta maka rundunar a kotu, ana zargin ta da yin harkalla da cuwa-cuwar daukar ma’aikata, ribbatar matasa, damfara da kuma yin sojan-gona.
An dai gurfanar da dakarun lafiya ne a bisa tuhumomi har guda 90, da zargin wala-walar kudi kan Akoh har naira bilyan 1.4.
Wannan zargi bai sa Akoh ya daina gudanar da al’amurrran dakarun ba, duk da dai ya musanta zargin da ake yi masa, ya na mai cewa bakin ciki da hassada da kuma bukule ne kawai wasu bangarori na hukumomin tsaro ke nuna masa.
RA’AYIN DAKARUN ZAMAN LAFIYA
Dakarun Zaman Lafiya sun maida martani dangane da kin sa wa dokar kafa ta hannu da shuagaba Muhammadu Buhari ya yi.
Da ya ke zantawa da manema labarai na Majalisar Tarayya, Dickosn ya ce matakin da Buhari ya dauka bai ba shi mamaki ba ko kadan saboda ba bakon sa ba ne.
“Bari na ba ku wani labari da ba ku sani ba. Jami’an tsaro ne da kan su a ranar 1 Ga Janairu, suka je suka samu Shugaba Buhari suka ce masa ai da a sake kudi wajen kafa wata rundunar zaman lafiya, gara ma a kashe kudin da za a kafa ta wajen kara inganta hukumomin tsaron da ake da su.”
“ Ni dai abin da na ke yi ina yi ne saboda taimakon akasarin matasan Najeriya. Amma daga abin da na ke gani, akwai makarkashiya a cikin shirin na kin amincewa da kafa rundunar.” Inji Dickon.
Discussion about this post