Kafin hargitsin da ya yi sanadiyyar kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Mohammed Yusuf da wasu daruruwan magoya bayan sa a Maiduguri, sunan Abubakar Shekau bai bi duniya sosai ba. An dai san shi a matsayin malami mai wa’azi da bada karatu ko fatawowi, kamar yadda Muhammaed Yusuf ke yi.
Sai bayan kashe Mohammed Yusuf ne, bayan da Shekau ya yi sanarwar karbar ragamar shugabancin kungiyar Boko Haram ne, wasu da dama su ka gane cewa ashe ma ya fi Moahmmed Yusuf zafi, watakila don ya na mataimaki kafin Shekau ya mutu, shi ya sa ba a rika jin sa sosai ba.
Kafin Mohammed Yusuf ya fara fada da jami’an tsaro, ya fifita yin amfani da harshen sa da kuma wa’azi a matsayin makamin da ya ke yi wa Nijeriya kan ta barazana.
Amma shi kuwa Shekau, bai tsaya wata-wata ba, sai ya kaddamar da yaki bagatatan da jami’an ‘yan sanda, sojoji, kai har ma da kasar gaba daya.
Irin makaman da Boko Haram su ka tanada ya sa tun da farko su ka gagari jami’an ‘yan sanda, yadda tilas sojoji suka karfi tarar aradun fada da maoya bayan kungiyar Boko Haram.
Ganin yadda yakin ya ki ci, ya ki cinyewa, a kullum Boko Haram na kai munanan hare-hare a fadin Arewacin kasar nan, har da Abuja, hakan ya haifar da babbar matsalar rashin tsaro a Arewa, musamman a jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Bauchi, Gombe, Kano, Kaduna har ma da Abuja.
Cikin watan Nuwamba, 2012, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta bayar da ladar zunzurun kudi har naira milyan 290 da duk wanda ya baar da bayanin inda Shekau ya ke a boye, har kuma aka yi nasarar cafke shi.
Maimakon Shekau ya shiga taitayin sa, sai ma ya kara bude wutar kai munanan hare-hare a cikin shekarar da aka bayyana ladar naira milyan 290 ga duk wanda ya yi silar kama Shekau.
Ganin yadda riikicin ya kara muni, kasar Amurka ta yunkuro a cikin watan Yuni, 2013, ta bayyana ladar makudan daloli har milyan 7 ga duk wanda ya yi sanadiayyar kama Shekau.
Makudan kudaden da Amurka ta yanka a matsayin lada, a yanzu sun kai naira bilyan biyu, idan aka canja su daga dala zuwa naira. Amma duk da wannan, har yau babu wanda ya kwarmata inda Shekau ya ke.
Ba mamaki, wannan zai iya zama hujjar da ake cewa a cikin Kamaru Shekau ya boye, ba a Nijeriya ba.
Sai dai kuma abin da ya fi daukar hankalin mutane da kuma jefa waswasi a zukatan jama’a, shi ne yadda rundunar sojojin kasar nan su ka rika bayyana cewa an kashe Shekau, ko kuma Shekau ya gudu, ba sau daya ba.
Ba sau daya ba kuma sai bayan an bayyana mutuwar sa, sai ya bayyana ya na gwasale gwamnati da jami’an tsaro.
Hawan Gwamnatin Muhammadu Buhari, an ga kwakkwaran canji matuka wajen dakile kaifi da dogon zangon da Boko Haram, ta yadda suka takaita kai hare-haren su a Maiduguri da Yobe kadai.
Nasarar da sojojin Nijeriya suka samu har suka kutsa Dajin Sambisa, ta kara karya lagon Boko Haram. Amma kuma kafin sannan sojojin sun sha nanata cewa an gama da Boko Haram gaba daya.
Ko a bayan wani harin baya-bayan nanan da sojoji suka yi nasarar kama manyan kayan yakin Boko Haram, sun bayyana cewa sun gama da Boko Haram, amma Shekau ya fito ya musanta cewa wai an kakkabe su.
To a satin da ya gabata, kuma sai ga sabuwar sanarwar cewa za a biya ladar naira milyan uku ga duk wanda ya bayyana inda Shekau ya ke har aka yi nasarar cafke shi.
Jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa, jama’a sun cika da mamakin yadda farashin Shekau ya fadi kasa warwas. A gefe daya kuma akwai masu fahimtar cewa an rigaya an kakkabe Boko Haram, saura ‘yan burbushi kawai.
Ba mamaki sojoji sun hakkake Shekau na fama da wani mummunan rauni, kamar yadda su ka yi bayani, ta yadda nan gaba ba zai iya ci gaba da shugabancin kai hare-hare da ya ke ta yi ba.
Sannan kuma mai yiwuwa akwai dalilin cewa mabiyan sa sun tarwatse, an kashe wasu, kuma an cafke su ko kuma sun mika wuya bayan sun ajiye makamai.
Ko ma dai me kenan, hakika sojojin Nijeriya sun taka rawar ganin samun nasarar da suka yi har ta kai mu a yau su na ayyukan raya karkara da suka hada da gyaran haya da kuma aikin gina rijiyar burtsattse a cikin tsakiyar Dajin Sambisa.
Mai yiwuwa shi ma Shekau din, za a iya cewa nesa ta zo kusa.