Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya bayyana cewa kafa dokar kiwon dabbobi a killace zai taimaka wajen kawo karshe rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Darius ya fadi haka ne da yake amsar bakwancin jakadan Amurika a Najeriya William Stuart a Jalingo.
” Idan dai ana so a kawo karshe wadannan rikice-rikice ya zama dole mu kafa wannan doka don zai taimaka wajen rage watangarerewa da makiyaya kan yi.
Daga karshe ya yi kira ga gwamnatin kasar Amurka da ta mara musu baya wajen samar da zaman lafiya a jihar da kuma kasa baki daya.