KANO: Ma’aikatan Hisba sun tarkata mabarata a titunan Kano

0

Jami’in hukumar Hisbah dake jihar Kano Dahiru Nuhu ya bayyana cewa cikin kwanaki 30, wato wata daya ma’aikatan sa sun tarkata mabarata 94 dake gararamba a titunan jihar.

Ya sanar da haka ne wa manema labarai a Kano inda ya kara da cewa sun kama mabaratan ne don karya dokar hana bara da suka yi.

” Hukuncin karya wannan dokar shine daure mabaraci a kurkuku har na tsawon watanni uku amma duk da haka mun saki mabaratan da muka kama domin mun gano cewa wannan shine karo na farko da suka fito bara.”

Nuhu ya ce sun kama 24 yara da manya 70 a tashoshin motoci da wuraren cin abinci.

Share.

game da Author