Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gama shiri tsaf don horas da likitoci 54 da ma’aikatan jinya 600 a jihar.
Ya fadi haka ne da yake amsar bakuncin shugaban asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina, Suleiman Muhammad tare da tawagarsa a Katsina.
Masari ya kuma kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da hada hannu da asibitin gwamnatin tarayya domin inganta kiwon lafiya a jihar.