Yunkurin kwace kujerar Sanata Jang ya haifar da sa-in-sa

0

Sanatan Jos ta Arewa, Jonah Jang ya yi sa-in-sa da Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Jos ta Kudu da ta Arewa, Edward Pwajok, dangane da muradin da dan majalisar ke da shi kuru-kuru na neman maye gurbin Jang a zaben 2019.

An samu sabanin ne bayan da sanata Jang kuma tsohon gwamnan jihar Filato ya furta a wani gidan radiyo cewa “kujerar samara ba kujerar matasa ba ce.”

Sai dai kuma wani hadimin Pwajok, Ayuba Pam, ya maida martani a ranar Asabar inda ya ce ai zaben 2019 babu ruwan sa da yawan shekarun mutum ko kuma kasancewar mutum matashi ne. Sai ya ce nagarta da halayen mutum su ne za su nuna makomarsa a zaben sanata a 2019.

Dama kuma a halin yanzu akwai fastar Hon. Pwajok ana ta raba ta, wadda ke nuna ya na harin kujerar sanata ta Arewa.
Ya ci gaba da cewa, “to abin da Jang bai karasa ba, shi ne sai ya fito ya shaida mana daga wace shekara mutum ke zama dattijo kuma daga wace shekara zuwa wace ce, ake samun matasa?”

Shi ma hadimin Sanata Jang mai suna Clinton Garba, ya bayyana cewa Sanata Jang ya hangi abin da ya hango shin ya sa ya fadi haka. Ya ce Jang mutum ne da ya ga jiya kuma ya ga yau, don haka ya na da gogewar da zai yi tsinkayen da ya yi.

Share.

game da Author