Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta tallafa wa yara marayu 100 wadanda suka rasa iyayen su sanadiyyar hare-haren Boko Haram a jihar Barno.
Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya yi wannan sanarwa ne a ziyarar da ya kai jihar Barno ranar Juma’a, tare da wasu sarkunan gargajiya daga jihar.
Gwamna Ganduje da tawagarsa sun ziyarci sansanin ‘yan gudun hijra na Dalori-1 inda suka bada gudunmawar Naira miliyan 20 da barguna 100,000 domin mazauna sansanin.
Bayan haka gwamna Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano za ta dauki nauyin yara 100 domin biya musu kudin karatu a jihar Kano.
” Marayun da muka dauka da wadanda muka zo mu kara sun zama ‘ya’yan jihar Kano sannan gwamnatin ta dauki nauyin biyan kudaden makarantan su har zuwa jami’a.”
” Mun yi haka ne domin mu agaza wa gwamnatin jihar Barno ganin cewa wannan hare-hare na Boko Haram ba su kadai bane za a bar su da hidimar wadanda abin ya faru dasu.”
A karshe gwamnan jihar Barno Kashim Shetima ya jinjinawa gwamnatin jihar Kano, kungiyoyi masu zaman kansu da shugabanin addinai saboda tallafin da suke ba gwamnatin jihar.
” Lallai Kano ta nuna mana cewa mu nasu ne kuma suma namu ne musamman a wannan lokaci da ta share mana hawaye.”