Kungiyoyin malaman jami’o’i mallakin gwamnatin jihar Nasarawa sun janye yajin aikin da suka shiga ranar 23 ga watan Fabrilu.
Shugaban kungiyar Ariks Samuel-Bashayi ya sanar da haka wa manema labarai a kwalejin koyar da malunta dake Akwanga bayan zama na gaggawa da shugabanin kungiyoyin suka yi a yau.
Samuel-Bashayi y ace sun dakatar da wannan yajin aikin ne saboda rokon da gwamnati da masu ruwa da tsakin jihar suka yi game da janye yajin aikin.
” Ko da yake gwamnati bata biya bukatun mu ba amma rokon su da suka yi game da janye yajin aikin ya bada sararin tattauna biyan bukatun mu.”
” A dalilin haka ne nayi kiraga ga duk wani malamain kwalejin koyar da malunta dake Akwanga , kwalejin koyar da aiyukan noma dake Lafia da jami’ar kimiya na jihar Nasarawa dake Lafia da su dawo aiki.
Bukatun kungiyoyin sun hada da rashin biyan malamai albashi, rashin karin girma wa malamai, rashin biyan su alawus da sauran su.