Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya bayyana cewa za a sake tantance wadanda sunayen su ya fito a aikin malunta na jihar su 15,000 da ‘yan kai.
Ya fadi haka ne ranar Juma’a da yake tattaunawa da kungiyoyin kawo ci gaba da masu ruwa da tsaki a jihar kan hanyoyin da za a bi wajen tantance malaman.
Ya ce same tantance wadannan malamai ya zama dole ganin cewa an gano sunayen wadanda aka kammala tattance su a farko da yawa ba su da kwarewa a aikin malunta.
El-Rufa’I ya yi kira ga kwamitin tattance malaman da su tabbata sun yi aiki mai nagarta, Kada su nuna bambamci ko kuma son kai.
” Aikin ku ne ku tankado mana wadannan malaman da basu da kwarewa a aikin koyarwa, kada ku yarda sunayen su ya fito cikin jerin sunayen wadanda suka kware.
Domin gudun Kada a sake maimaita irin haka gwamnati ta kafa kwamitin mutum uku da za su yi aiki da hukumar tantance malaman firamare din domin gudun aukuwar irin haka nan gaba.
Shugaban hukumar SUBEB, ya ce za a fara tantance malaman ne daga ranar Talata mai zuwa sannan za a tantance mutane 70 a duk rana.
Wandanda aka gamsu da su ne za a basu takardun daukan aikin malunta a Jihar.
Discussion about this post