Wasikar Obasanjo: Sakon ko Dan-sakon? Daga, Dr. Ibrahim Siraj Adhama

0

Idan akwai wani batu da ya mamaye fagen siyasa a Najeriya a makon da ya gabata bai wuce wasikar da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya rubutawa Shugaba Muhammadu Buhari ba.

A ranar Talata (23/1/18) ne aka samu bayyanar wannan zungureriyar wasika a kafofin yada labarai dauke ne da kakkausar suka ga gwamnatin Buhari da kuma salon mulkinsa sannan ta kunshi bayar da shawara gareshi kada ya tsaya takara a 2019 don yin mulki karo na biyu. Wannan wasika ta yamutsa hazo kwarai da gaske kuma har yanzu ana cigaba da samun martini daga bangarori daban daban na masu goyon baya da marasa goyon baya.

Tun samun bullar wannan wasika ra’ayin ‘yan Najeriya ya rabu biyu tsakanin masu ganin cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta tsaya ta kalli wasikar da abin da ta ke dauke da shi na bayanai musamman wadanda akwai kanshin gaskiya a cikinsu da ba tare da damuwa da wanda ya rubutata ba da kuma wadanda su ke ganin marubucin za a kalla wanene shi kuma ko ya dace ya rubuta irin wannan takarda ko bai dace ba.

Masu wannan ra’ayi su na ganin cewa a matsayin tsohon shugaba Obasanjo na wanda ya mulki Najeriya tsawon shekaru takwas kuma ya kasa tsinana abin a zo a gani a wadannan shekaru bai kamata a ce shi ne zai aiko da irin wannan sako ba. Sun ci gaba da tuna mana yadda Obasanjo a mulkin sa na shekaru takwas ya kasa magance ko daya daga cikin muhimman matsalolin Najeriya kamar wutar lantarki, samar da abubuwan more rayuwa, farfado da matatun mai, baza komar tattalin arziki da yayeshi daga dogaro bisa kan man fetur kadai da sauransu.

Sannan sun yi nuni da irin yadda cin hanci yai katutu ta yadda har shi ma Obasanjon bai kubuta daga zarg bai. Akwai ma maganar kashe kashen dauki-dai-dai da aka dinga yiwa fitattun ‘yan siyasa sannan ga rikice-rikicen kabilanci da na addini da akai ta fama da su a mulkinsa kamar a Kaduna, Shagamu da Yelwan Shendam wadanda su kai sanadiyyar salwantar rayuka masu yawa. Ga kuma rigima tsakanin Obasanjo da majalisun kasa musamman ta dattijai wacce yai ta canjawa shugabanni karfi da yaji da rikicinsa da shugabanni daban-daban na jam’iyyarsa ta PDP wadanda su ma ya dinga tursasa musu sauka da karfin tsiya saboda sun saba da shi a wani al’amari.

Sannan uwa uba ga yunkurinsa na canza tsarin mulkin Najeriya don zarcewa a kan mulki karo na uku har ta kai ya na ba da cin hanci na makudan kudade ga majalisa kamar yadda akai holen irin wadannan kudade buhu-buhu a majalisa a wancan lokaci. A ganinsu Obasanjo ya gaza a mulkinsa kuma ya tafka ta’asa iri-iri kuma bai dace a ce shi ne zai dagawa wani shugaba kara ba.

Masu ra’ayin a dubi sakon Obasanjo suna ganin cewa tsohon shugaban na da ‘yanci a matsayinsa na dan kasa ya bayyana ra’ayinsa akan kowanne irin lamari da ya shafi Nigeria musamman abin da ya shafi gwamnatin da ya taimaka wajen samun nasararta. Kuma ko ba komai su na ganin akwai kanshin gaskiya a zarge-zargen da ya yi a wasikar tasa. Misali Obasanjo ya koka akan matsanancin halin rayuwa da ake ciki a kasa ga yunwa da talauci da rashin aikin yi sun yi katutu a cikin al’umma.

Haka nan ya koka akan yadda ake ganin Shugaba Buhari ya mika ragamar tafiyar da gwamnati ga wadansu mutane da ba su talaka ya zaba ba hasali ma bai sansu ba amma ga shi su na yin yadda su ka ga dama. Akwai kuma zargin wariya wajen nade-nade da bayar da mukamai a gwamnati inda ake zangin Shugaba Buhari da fifita abokansa da yankin day a fito wanda hakan na kawo matsala ga hadin kan kasa baya ga zargin ba da mafaka ga makusantansa wadanda ake zargi da aikata ba daidai ba ko ma cin hanci da rashawa.

A gurin wadannan mutane gaskiya ko ta kare ce dole a ba shi kuma Shaidani ma akan dace ya fadi gaskiya. Saboda haka su na ganin ya wajaba a kalli wannan sako da idon basira kuma ayi aiki da shi a matsayin gyara kayanka.
Tabbas wadannan bangarori su na da hujjoji masu karfi ta yadda zai yi wahala a yi watsi da kowanne ra’ayi. Sanannen abu ne cewa dole mai bunu a gindi ba ya kai gudunmawar gobara sannan wanda zai yi magana akan gyara ya kamata ya zama shi ma gyararre ne. A bisa wannan Obasanjo ba shi da cancantar ya zo da maganganu irin wadannan duba da cewa kusakuran da ya tafka sun fi muni akan wadanda ya zargi Shugaba Buhari da su a wasikarsa. Kuma a hankalce ana sa ran duk wanda zai yi wa’azi ko gargadi ayyukansa su kasance sun dace da wa’azinsa.

Samun hakan ya na karawa masu saurare karbar sakon da ya zo musu da shi kamar yadda rashin hakan ke sawa su yi watsi da shi bisa tunanin shi ma mai maganar ba da gaske ya ke ba. Sai dai kuma a gaskiyance akwai gagarumar matsala mutum ya yi watsi da shawara da aka bayar ta gaskiya saboda tunanin wanda ya bayar da shawarar bai cancanta ya bayar da irin wannan shawara ba. Wannan ya sa ya zama wajibi gwamnatin Shugaba Buhari ta saurari shawarwarin da aka ba ta da kunnen basira da niyyar gyara abin da za ta iya gyarawa. Izuwa yanzu dai Jama’a da dama dai sun yaba da martinin da gwamnati ta bayar ta hanyar bayanin irin ci gaban da ta samar kuma da amincewa cewa akawi matsaloli a wasu gurare da su ke bukatar kara zage dantse, ba tare da kausasa lafazi ga Obasanjo ba kamar yadda aka saba a baya ba.

Game da babbar takaddamar da Wasikar Obasanjo ta jawo na cewa kada Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara ya hakura haka ya koma gida, ni a ganina wannan kiran bai dace ba. A matsayinsa na dan Najeriya Shugaba Buhari ya na da ‘yanci ya tsaya takara kamar yadda tsarin mulki ya amince masa. Bisa wannan bai kamata Obasanjo ya yi wannan magana ba, musamman ganin cewa shi har karo na uku ya so ya shugabanci Najeriya ta hanyar canza Tsarin Mulkin Najeriya. Ya dace a kyalewa kowa damarsa da tsarin dimokradiyya ya ba shi, ya rage na ‘yan Najeriya su yi hukunci. Dimokradiyya ta wanda ya fi jama’a ce kuma jama’a su na da ‘yancin su za bi wanda su ke so. Idan sun ce Shugaba Buhari ne zabinsu dole a hakura idan kuma sun ce wani ne shi ma Shugaba Buhari dole ne ya hakura.

Dr. Ibrahim Siraj is from the Department of Mass Communication, Bayero University, Kano and can be reached at adhamai@yahoo.com and isiraj.mac@buk.edu.ng

Share.

game da Author