Jami’in hukumar kare haddura ta kasa FRSC reshen jihar Kaduna Umar Ibrahim ya bayyana cewa akalla mutane 20 ne suka rasa rayukan su a hadarin mota da aka yi a hanyar Abuja zuwa Kaduna da yammacin Lahadi.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da kamfani dillancin labaran Najeriya a Kaduna inda ya kara da cewa hadarin ya auku ne a daidai Dutse.
Ibrahim yace hadarin ya auku ne yayin da wata mota kirar Tayota HAICE wacce ke daukar mutane 16 amma ta dauki mutane 30 da kaya take kokarin komawa dayan hannun ne wata motar DAF fara ta zo a guje ta daketa.
Sakamakon haka mutane 17 suka mutu nan take sannan ma’aikatan FRSC suka kwashi mutane 10 zuwa asibiti.