El-Rufai, dace ko an dace? Daga Mahmood Muhammad

0

Ko da yake mutane da yawa basu saba da irin salon gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ba, sai da akwana a tashi yar fara tana ta nunawa.

An saba da ayi ta watanda da kudaden gwamnati, ‘yan siyasa na zuba abin da suka ga dama a jihar ba tare da wani ya isa ya ce musu tak ba, sai gashi Allah ya amsa addu’ar talakawan jihar ya basu Malam Nasir El-Rufai.

Rabon da Kaduna ta ga irin ayyuka da canje-canje na ci gaba a jihar, wasu masana sun ce tun zamanin Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello, lokacin da Kaduna ke hedikwatar Arewa sai ko gwamnan Balarabe Musa.

Yanzu a jihar Kaduna, gwamnati na aiki ne babu kakkautawa, duk kauyen da ka shiga za ka ga wani aiki da gwamnati ke yi a wannan kauye.

Cikin shekaru biyu kacal gwamnatin Kaduna ta samar wa ‘yan jihar ayyukan yi sama da 4000, da ya hada da aikin Kastelea, da na malunta wanda su aka fara dauka daga hawan sa.

Shirin wannan gwamnati na Mal. Nasir El-Rufai shiri ne na gyara Kaduna da jikoki za su mora.

Bayan sallamar dakikan malamai da gwamnan yayi, mutanen jihar suka fara korafe-korafe wai basu yarda da haka ba bayan kashi 99 bisa 100 na su masu korafe-korafen ‘ya’yan su ba su makarantun gwamnati.

Gwamna El-Rufai ya jajirce sannan ya kafe a cewa bazai dawo da dakikan malaman. Hakan yasa wasu da suke adwa da gwamnatin a siyasance da akidance suka wasa wukar su suka dinga zuga kungiyoyin malamai da na Kwadago inda suka kira zanga-zanga sannan suka shiga yajin aiki.

Duk da irin wadannan adawa, gwamnan Nasir bai karkata daga abinda ya sa a gaba ba na samar wa talakawan jihar da ‘ya’yan su ilimi mai nagarta.

Sannu- sannu kuwa, bayan haka kungiyar malaman suka fahimci abinda suke yi ba daidai bane suka gane cewa makiyan su ne ke suga su domin ganin gwamnatin Nasir bai cimma burin su.

Idan har za a yi wa gwamna Nasiru adalci, cikin mutanen da suka rubuta jarabawar gwaji, sama da 10,000 sun ci jarabawar, sannan yace zai dau Karin malamai sama da 25,000 kari. Wanda hakan ya kusan rubanya wadanda suka fadi jarabawar idan ka hada da wadanda ake ta dauka tun bayan hawan sa gwamnati a 2015.

Idan Ka duba fadin jihar zaka ga ko ina ana aiki, babu birni babu karkara. Idan badun matsalar kudi da ake fama da shi a kasar nan ba da wasu aiyukan sun zama labari, amma duk da haka bai kasara ba, yana ta kokarin ci gaba da ganin ayyuka suna ci gaba a hankali a hankali.

Babu wani fanni a jihar Kaduna da gwamantin El-Rufai bai ce mata gani na zo ba.

Wani abu da ke dada seta gwamnatin Mal. Nasiru El-Rufai shine tarayyar sa da mai bashi shawara kan harkar Siyasa, wato Mal. Uba Sani.

Mal. Uba Sani da akeyi wa lakabi, sarkin aiki, mutum ne da a duk inda ka ganshi yana aiki ne domin ci gaban kaduna da gwamnatin gwamna Nasir El-Rufai.

Uba Sani bai bari siyasar ‘yan siya sun karkatar shirin gwamnati ba musamman wajen daukar lodin adawar siyasa da akeyi wa gwamnatin ba. Ya maida hankali wajen ganin abin da akasa a gaba shine aka mai da hankali akai. Duk wani shiri da makirci na siyasa ya tabbatar da bai kawo wa gwamnan jihar ko aiyyukan da aka sa a gaba ba cikas ta ko wani hanya.

Dama can jarumi ne, sannan gogaggen dan siyasa mai kare hakkin mara sa galihu da taimakon talakawa.

Wannan hadi nasa da gwamna El-Rufai sai yayi daidai.

Yanzu kamar yadda kowa ya sani, malamai sun hakura, sun koma aiki, sannan gwamnati bata bari abubuwan da sukayi a da ya bata mata shiryeshiryen ta ba.

Nasir El-Rufai ya lashi takobin gani jihar Kaduna sai ta zamo abin koyi da sha’awa ga duk ‘yan Najeriya.

Share.

game da Author