Obasanjo zai kafa kungiya don fatattakar Buhari a Ofis

0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na hado kan yan siyasa don kafa wata kungiya don ganin ko ta halin kaka Buhari bai koma kan karagar mulki ba a 2019.

Kusan duka wadanda Obasanjo ya tuntuba kan wannan shiri ta sa sun rattaba hannun nuna goyon baya ga wannan shiri da zai ceto Najeriya, wanda ba iri daya yake ba da manufofin jam’iyyar PDP ko na APC.

Obasanjo yace jam’iyyun APC da PDP duk watangaririya kawai suke yi.

Kwakkwarar majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa a zaman yanzu gwamnoni bakwai, sanatoci 20 da mambobin majalisar tarayya 100 sun rigaya sun sa hannunn amincewa shiga jirgin ceto Najeriya da Obasanjo zai gina nan ba da dadewa ba.

Alamomin Obasanjo ya fara gajiya da salon takun mulkin Buhari, wanda shi Obasanjo din ya mara wa baya a zaben 2015, sun fara fitowa fili ne a farkon wannan wannan watan a wani taro da Obasanjo ya yi jawabi a Jami’ar Oxford ta Ingila.

A jawabin nasa, Obasanjo ya yabi yadda wasu shugabannin Afrika suka farfado da tattalin arzikin kasashen su, amma sai bai yi maganar Najeriya ba.

Sai dai kuma a lokacin da aka tambaye shi abin da zai ce dangane da Najeriya, sai Obasanjo ya ce ai lokacin da zai yi magana kan Najeriya bai yi ba tukunna.

Majiyar da ke da kusanci da Obasanjo, ta kuma shaida wa PREMIUM TIMES cewa tuni Obasanjo ya yi taro da tsoffin shugabannni, tsoffin gwamnoni da manyan tsoffin ‘yan majalisar tarayya daga bangaren sanatoci da kuma na wakilai.

Share.

game da Author