Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa a cikin 2017, ta yi rashin ma’aikata har 85, wadanda suka mutu a cikin shekarar.
Shugaban Hukumar ne, Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana haka. Ya na mai cewa wannan dalili ne ya sa INEC ta saka aikin gina asibitin da zai rika duba marasa lafiya a cikin gaggawa a hedikwartar hukumar da ke Abuja.
Yakubu ya ce an saka wannan aikin a cikin Kasafin Hukumar na 2018.
Yakubu ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga Kwamitin Majalisa Kan INEC a jiya Laraba, dangane da dalilin da ya sa za a gina wurin duba marasa lafiya a hedikwatar hukumar, a cikin wannan kasafin kudi.
Ya ce an yi wannan tunani ne domin a rika gaggauta duba marasa lafiya da kuma kauce wa yawan mamace-macen da ake yi, ganin cewa za a rika gaggawar sanin halin da ma’aikatan hukumar ke ciki.
“Ina so na jawo hankular sanatoci cewa ana samun yawan mace-mace a INEC. Cikin 2017 kadai mun rasa ma’aikata 85, wasu ta dalilin hadurra, wasu da dama kuma rashin lafiya ce. Dalili kenan mu ka son kafa wurin duba marasa lafiaya a cikin hedikwatar hukumar.
“Misali, wasu ma’aikatan mu haka kawai su ka yanke jiki a cikin hedikwatar mu, suka fadi. Sai muka fahimci cewa ana fuskantar wadannan matsaloli ne, saboda wasun mu ba su yawan auna lafiyar su, musamman auna jinin su da sauran gwaje-gwaje. Shi ya sa muka yi tunanin kafa wurin duba marasa lafiyar.”
Da ya ke sake bayyana dalilin su na a kafa wurin rainon yara a cikin hedikwatar INEC, Yakubu ya ce sun yi haka ne domin a rage wa ma’aikatan hukumar mata marasa karfin daukar hayar masu rainon jinjiran su. Ya ce za a giggina su ne a kowace jihohin kasar nan.