2019: Shin ko ‘SAK’ zai sake tasiri?

0

A fadin Arewacin kasar nan, an yi ittifaki da cewa duk wani wanda aka zaba mukamin siyasa, ko a matsayin Sanata, Gwamna, Dan Majalisar Tarayya da na Jihohi, idan dai a karkashin APC ka ci zabe, to kowa gani ya ke ka ci albarkacin ‘Sak’ ne.

Sak dai kalma ce da aka kirkiro, wato duk wanda zai zabi Buhari a zaben 2015, to idan ka na kishin sa a zuci, to duk wani wanda za ka dangwala wa kuri’a, ya kasance jam’iyya daya ya ke da Buhari, ko ma wane ne, kuma komin irin nagarta da cancantar sa, ko akasin haka.

“Duk mai son uwa, ya so dan ta.” Haka aka rika yayatawa a lokacin guguwar Buhariyyar zaben 2015. Wato ba ka cika dan Buhariyya, sai ka yi ‘Sak’ a lokacin zabe.

Bayan nasarar Buhari da saki daya, an rika yayatawa a kafofin sadarwa na soshiyal midiya cewa dan Buhariyya bai cika mai kishi ba, har sai ya zabi gwamnan APC, don kada gwamnonin adawa su hana Buhari aiki idan ya hau shugabanci.

Dama kuma a zaben sanatoci da na majalisar tarayya, an rika cewa a zabi APC, don kada masu adawa a majalisa su yi fifikon da za su hana shugaban kasa aiki.

Sai dai kuma tun tafiya ba ta yi nisa ba, yawancin mabiya akidar ‘SAK’ suka fara sakankancewa da yawan wadanda suka zaba, duk zaben-tumun-dare suka yi. Tun ba a haura shekara daya da mulki ba, an ga yadda talakawa suka fara hasala, su na bin wakilan sun a APC da jifa, saboda haushin su da kuma da-na-sanin zaben su da suka yi.

Yanzu haka dai an kai shekara uku da yin zaben 2015, kuma kadan ya rage Shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekara uku a kan mulki. Tuni masu ra’ayin takara sun fara fitowa da fastoci domin gwada sa’ar zaben 2019.

Abin tambaya a nan, me ya sa aka daina zancen ‘SAK’?

1 – Shi kan sa Shugaba Buhari na da masaniyar yadda wadansu ya ja a jika suka kasa tabuka abin a yaba. Sannan kuma ya na sane da yadda ake zargin makusantan sa da harkalla da karma-karma. Ya kuma san irin yadda talakawa ke jin haushin wasu jiga-jiga gwamnatin ta sa. Da wuyar gaske a wannan karon a bi umarnin sa, idan ya fito takara ya yi kururuwar a yi ‘Sak.’

2 – A soshiyal midiya a kullum magoya bayan APC na ta nanata cewa a 2019 ba za su yi ‘sak’ ba, sai sun duba, sun darje.

3 – Hasalallu sosai na ta rubuta cewa ko Buhari ne ya ce a yi ‘Sak’, su ba za su yi ba.

4 – Sau da yawa da an tura hoton wani sanata ko dan majalisar tarayya a soshiyar midiya, za ka ga da yawan wadanda suka zabe shi a mazabar sa, su na rubuta cewa, ‘ya ci taliyar karshe’, wato daga 2019, za su kulle masa kofar shan romon mulki a Abuja.

5 – Alamomi na nuna cewa babu batun ‘Sak’ a kamfen din APC a 2019. Da yawan talakawan Arewa na jin haushin yadda ake yawan tula wa gwamnonin su kudi, fiye da lokacin gwamnonin Jonathan, amma kuma biyan albashi ma sau da dama sai an kai ruwa rana. Har yanzu akwai jihohin da ake tata-burzar biyan albashi, ballantana kudaden alawus-alawus da na fansho da garatuti.

7 – ‘Sak’ ba za ta yi tasiri a kan gwamnonin da talakawa ke ganin sun zabe su don su share musu hawaye ba, amma tun da farkon hawan su, sai suka dora harsashin gwamnatin su kan gallaza wa talakawa azaba.

8 – Za ka rika gani a soshiyar midiya matasa na rubuta: “2019: Halin ka ya kai ka!’’ A nan su na nufin sun sa lauje sun datse igiyar “SAK’’ a akidar su ta mabiya Buhariyya, sai wanda su ke so za su zaba.

9 – Wata babbar matsala a nan ita ce, akwai alamomin za a yi ‘anti-party’, wato dan wannan jam’iyya ya zabi waccan jam’iyya a duk inda aka tsaida masa dan takarar da ba ya so. Kenan akwai aiki ja ga shugabannin jam’iyyar APC na kasa, na shiyya, na jiha da na kananan hukumomi, kai har ma da na mazabu. Idan su ka tsaida wa magoya bayan su ‘baubawan-burmin’ da ba su kauna ya wakilce su, to ‘anti-party’ fa za a yi.

10 – A zaben sanatoci, wakilai na tarayya da na jihohi ne hasalallun ‘SAK’ za su fi huce-haushi. Domin da yawan su sun tafi a kan wakilan sun a Abuja ba za su koma majalisa ba, sai dai su kalle ta a talbijin daga 2019. Hakan na da nasaba da yadda suke ganin yawancin abin da Buhari zai nemi a yi masa a majalisa nan take, to sai ya yi ‘yar-murya, roko da durkuso kafin a biya masa bukatar tasa.

11 – Akwai kuma batun jin haushin cewa daga cikin masu gasa wa Buhari gyada a ka, su na caja masa kwakwalwa, har da wakilan su na APC da suka shiga majalisa albarkacin inuwar Buhari da kuma tubarrakin siyasar sa.

Share.

game da Author