Obasanjo ya caccaki gwamnatin Buhari, yace kada ya kuskura ya sake takara

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya gargadi shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura ya ce zai sake fitowa takarar shugabancin Najeriya a 2019.

Obasanjo ya ce ya hakura hakannan yabi sahun su dattawa suna ba da shawara a bayan fage.

Obasanjo ya kara da cewa duk da ya san cewa Buhari na da rauni a musamman fannin tattalin arzikin kasa, ba a nan bane kawai ya bashi kunya har da wasu fannoni da da ana tunanin idan shi Buhari ya hau zai gyara su amma jiya iyau.

Yace bayan rufe idanuwar sa da yayi wajen yaki da cin hanci da rashawa da ya dabaibaye gwamnatin sa wanda hakan yasa ake masa ganin kuru-kuru yana take nasa ne ya fallasa na wasu.

Sannan ya ce abin da ya kara bashi haushi da gwamnatin Buhari shine yadda ya bari rikici tsakanin Makiyaya da manoma yayi kamari a kasar nan sannan kuma duk da haka wasu gwamnoni a hakane suke fitowa wai sun amince masa da ya sake fitowa takara.

Yace gazawar Buhari ba a nan ya tsaya ba, har da kulle-Kurciyar da akayi tayi kan badakalar Maina, da har yanzu ba a fito an baiyanawa ‘yan Najeriya ainihin abin da a ke ciki ba sai boye-boye kawai ake tayi na rashin gaskiya.

“ A wannan Mulki, Buhari ya dada raba kawunan ‘yan Najeriya ne, inda bambance-bambance tsakanin ‘yan kasa ya dada bayyana, sannan babu tausayi a tsakanin Kabilu da mutanen kasa.

“ Wani abin takaici kuma shine yadda a kullum gwamnatin Buhari ke jingina rugujewar darajar naira ga gwamnan babban bankin Najeriya ana cewa wai gwamnatin baya ne ta lalata komai. Kada kuyar da wani ya zo ya cuceku, shi dama tattalin arzikin kasa da siyasa kamar Hassan ne da Hussaini, idan siyasa tayi kyau, ita ma zata yi kyau. Da komai lafiya a Najeriya, ay da ba a nace sai Buhari ya zama shugaban kasa ba. An zabe shi ne dama don ya gyara ba yayi ta dora ma wani laifi ba.

Sannan yace Buhari da jam’iyyar sa basu da amsa ga matsalolin da Najeriya ta shiga a yanzu.

“ Buhari bashi da Isasshen lafiyar da zai iya fafatawa da matsaloli da hayaniyar Najeriya a yanzu, haka jam’iyyar sa ta APC. Buhari ya hakura kawai idan ya kammala sauran shekarun da ya rage masa a mulki ya koma ya kula da lafiyar sa. Kada ya yarda yace zai biye wa wadanda suke zuga shi cewa sun fi son sa fiye da Allahn da suke bauta wa, wadanda suke zuga shi suna cewa idan bashi babu Najeriya.”

“ Buhari ya hakura, ya ajiye mulki idan wa’adin sa yayi a 2019, ya dawo ya huta wa ransa, ya samu ya dan natsa, jikin sa ya murmure. Sannan ya dawo ya shiga cikin jerin tsoffin shugabanni na da da za su ci gaba da ba da shawara domin ci gaban kasa Najeriya.

“ Ina rokon Buhari da ya hakura hakannan, ya dawo ya huta wa rayuwan sa, shekaru sun yi nisa yanzu. Ya hakura hakannan. Ina yi masa fatan Alheri sai dai ba dole bane Buhari ya bi shawara ta, sai dai ko ya bi ko kar yabi, Najeriya na bukatan ta ci gaba.

Share.

game da Author