Sanatan da ke wakiltan Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, Danjuma Laah ya shaida wa gwamnatin tarayya cewa mazabar sa bata da filayen da za ta iya badawa don kirkiro burtuloli da dangwali wa fulani makiyaya don shanun su a yanki Kaduna ta Kudu.
Laah ya ce su a shirye suke su bada filaye don gina jami’o’I, ma’aikatun gwamnati, da duk wani abu da zai amfani jama’a ba mika filayen ta don kirkiro wuraren kiwon shanu ba.
Idan ba a manta ba ministan aiyukkan gona Audu Ogbeh ya sanar da cewa jihohin yankin arewacin kasar nan da suka hada da Adamawa, Kano, Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi, Nasarawa, Plateau, Bauchi, Gombe, Borno, Jigawa, Yobe, Niger, Kogi da Kwara sun amince su bada filaye domin kirkiro irin wadannan wurare domin kiwon shanu wa makiyaya.
Ya ce makiyayan nan attajirai ne wanda ke da kudaden da za su iya siyan filaye domin shanun su.
Ya kara da cewa a yanzu haka akwai kebabbun filaye da aka ware don kiwon shanu wanda an kwace daga mutanen kananan hukumomin Zangon Kataf da Kachia tun a shekarun baya.
” Saboda haka jihar Kaduna ta bada filaye da dama wanda ya kai hekta 32,000 a Laguda da za a iya amfani da shi domin samar musu da wajen kiwo amma ba wasu sabbin filayen ba.”
Daga karshe Sanata Laah ya ce maimakon kwace wa manoma filayen don kafa wuraren kiwon shanu, tsaro ya kamata a samar wa mutane yanzu domin shin e suke bukata.