Fadar Shugaban Kasa ta maida wa Ghali Na-Abba martani

0

Fadar Shugaban Kasa ta yi kira ga tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na-Abba, ta ya sake duba da idon basira ya kalli ayyukan cigaban da gwamnatin Muhammadu Buhari ta aiwatar daga lokacin da aka zabe ta zuwa yau.

Babban Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Yada Labarai, Garba Shehu ne ya yi wannan kira a cikin wata takarda da ya fitar a jiya Litinin, a Abuja.

Shehu ya yi wannan martani ne dangane da kakkausan furucin da ya Ghali ya yi wa Buhari inda ya zarge shi da cewa bai iya tafiyar da mulki ba, don haka ba zai bata lokaci ya goya masa baya a zaben 2019 ba.

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Ghali Na-Abba, ya ce babu wani abin arzikin da mulkin Buhari ya kara wa kasar dimokradiyyar kasar nan.

Sai dai Garba Shehu ya roki Ghali da ya tsaya ya yi duba ga irin dimbin ayyukan alherin da ya ce mulkin Buhari ya samar wa kasar nan, daga 2015 zuwa yau.

Shehu ya nusar da Ghali cewa tattalin arzikin Nijeriya ya balbalce, amma zuwan Buhari ya sa an saisaita tattalin arzikin.

Ya kuma bada misali da tsaro, biyan kudin fanshon ‘yan sanda, karfin takardar naira, yalwar noma da sauran ayyukan da ya zayyana a cikin takardar martanin da ya yi wa Ghali.

Ghali dai ya nuna a fusace cewa ya sadakad cewa Buhari ba zai kulla abin kirki ba. Akwai inda ya bada labarin yadda suka karke a wani zama da suka yi a kebance:

“Mun yi wani zama da shi, na ce masa a gaskiya fa ana korafi da gwamnatin nan, kuma jama’a su na fama da kunci. Sai Buhari ya ce min, ‘e kwarai kuwa an yi fama da kunci, amma tun da aka zabe ni, ai alama ce ta cewa an fita daga wancan halin da ake ciki a da.’ A zuciya ta na ce lallai mutumin nan ya yi nisa……”

Share.

game da Author