Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Mahmood Yakubu, ya kara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa duk wanda suka zaba a 2019 da sauran zabukan gaba, shi INEC za ta bayyana a matsayin wanda ya yi nasara.
A wani rahoto da INEC ta buga a shafin ta na yanar gizo, Yakubu ya bada wannan tabbacin ne Taron Shekara-shekara na 15, wadda jaridar Daily Trust ta shirya a jiya Alhamis a Abuja.
Shugaban Wayar da Jama’a a Kan Mallakar Rajista, Solomon Soyebi ne ya wakilci Yakubu a wurin taron.
Ya ce a kullum ana samun ci gaba mai ma’ana sosai a wajen tafiyarwa da gudanar da zabe tunda Yakubu ya zama shugaban hukumar.
Shugaban na INEC, ya bayyana cewa zuwa makon da ya gabata, akalla mutane milyan 74 ne suka mallaki rajistar zabe.
Ya na mai karawa da cewa nan da shekara ta 2019, adadin zai iya kai miliyan 80 zuwa miliyan 85, saboda aikin ci gaba da sabunta rajista da ake ta yi a zaman yanzu a dukkan fadin kasar nan.
Ya jaddada aniyar INEC wajen tsayawa tsayin-daka ta yi aiki a ranakun da ta bayyana a cikin jadawalin shirye-shiryen zaben na 2019.
A karshe, Yakubu ya yi kira ga kafafen yada labarai da su rika tuntuba domin su tabbatar da sahihancin labaran da za su rika bugawa, domin hakan inji shi, zai rage yawan labaran karairayi da soki-burutsu da ke yawo a yanar gizo.