Kamfanin Mai na Kasa, NNPC, ya bayyana dalilin sa na biyan kudin tallafin man fetur ba tare da neman yarjewa ko amincewar Majalisar Tarayya ba.
Manajan Darktan PPMC, Umar Ajiya ne ya bayyana cewa dokar da ta kafa PPMC, doka ce mai zaman kanta, wadda NNPC ke aiki da shi ko da umarni ko ba umarnin Majalisar Tarayya.
Ya ce kamfanin PPMC reshe ne na NNPC, wanda ke tabbatar da cewa an samu wadataccen man fetur a kasar nan da zai wadaci hatta masana’antun ta.
“Mu dai a wurin mu ba ma bada da tallafi, ba mu san da tallafi ba, saboda baya cikin kasafin kudi, amma dokar kasa wadda ta kafa NNPC, kuma Majalisar Tarayya ta san da hakan, cewa mu na da ‘yancin yadda za mu rika tafiyar da ayyukan mu kuma mu dawo da kudaden mu cas-da-cas.