Wasu mahara dauke da bindigogi da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne, sun kai hari a wata supermarket a Katsina, inda har suka kashe wani dan sanda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Isa Gambo, ya ce an kashe jami’ain tsaron mai suna Ibrahim Batsari, kuma suka arce da bindigar sa, bayan sun kashe shi.
“Sun kashe jami’in dan sandan da misalin karfe 8 na dare a ranar Laraba, yayin da ya ke aikin sa na dare kusa da Wapa Supermarket, wadda ke kan titin IBB Way, a cikin Katsina.” Inji Gambo.
Ya ce jami’an suv na nan sun sha alwashin kamo ‘yan fashin. Ya kuma roki jama’a duk wanda ya ji kishin-kishin na inda barayin suke, to ya gaggauta sanar musu.
Wani da aka yi fashin a kan idon sa, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa, dan sandan na aikin sintiri ne a can kusa da kantin, sai ya ce bari ya je ciki ya kai wayar sa a yi masa caji.
Ya ce barayin sun hangi dan sanda dauke da bindiga, kawai suka bude masa wuta, suka dauke bindigar.