Imanin Obasanjo bai kai yi wa wani wa’azi ba, inji Fayose

0

Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose, ya bayyana cewa ba daga bakin mutum kamar Obasanjo ba ne za a ji nasiha ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Fayose ya yi wannan martanin ne ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, dangane da wasikar da ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, ya ke ba shi shawarar kada ya tsaya takarar 2019, domin bai tsinana komai a shekarun da ya yi ba.

Gwamnan ya ce Obasanjo na kokarin yin borin-kunya ne kawai, daga ribbatar ‘yan Najeriya da ya yi a baya, ya kai su ya baro su. Ya ce ai shi Obasanjon ne ma ke bukatar irin wannan shawarar, domin ya kai gargarar tsufan da ya kamata ya zauna a gida, ya daina cewa komai a batun mulkin Najeriya.

“Obasanjo da Buhari duk su kau ce su ba mutane wuri, yanzu yayin sabuwar tuwo ake yi, ba tsohon dumame ba.”

Ya ci gaba da cewa Obasanjo ne ya shige gaban ‘yan tuggun da suka kitsa hawan Buhari kan mulki, yanzu kuma ya dawo ya na kware masa baya, “ihu bayan hari kenan,”

“Obasanjo ne shugaban da ya kantara wa duniya karya cewa Buhari ne maganin duk wata matsala a kasar nan, ya sa aka mara masa baya.

“Saboda haka ‘yan Najeriya tuni sun rigaya sun yi wa kan su hisabin korar Buhari a zaben 2019, ba ma sai sun jira shawara, nasiha ko fatawa daga Obasanjo ba.”

“Tun mu na firamare mu ke jin sunan Obasanjo, ya kamata ya shige gida ya huta haka nan, domin a yanzu idan ‘yan Najeriya sun ji an kira suna sa, tsoki su ke yi.”

Share.

game da Author