Najeriya ta fada halin kakanikayi – Wike

0

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa ko shakka babu Najeriya ta fada halin kakanikayi a mulkin Buhari.

Wike ya fadi haka ne da yak e karbar bakuntar tsohon gwamnar jihar Jigawa Sule Lamido wanda dan takarar shugaban kasa ne a inuwar jam’iyyar PDP.

Lamido ya kai wa Wike ziyarar tayi ne da tallata kan sa kan abin da ya sa a gaba.

Sule Lamido yace yana da kwarewar da ake bukata don jan ragamar kasar nan saboda haka ne ya kai masa wannan ziyara domin samun karbuwa da neman goyon bayan sa.

Bayan ragargazar jam’iyyar APC da Wike yayi ya roki ‘yan takarar shugabancin kasar nan a Inuwar jam’iyyar PDP da su amince da sakamakon zaben fidda dan takaran shugaban kasa da jam’iyyar zata yi.

Share.

game da Author