ZAZZABIN LASSA: Hanyoyi biyar da Likita zai kare kan sa

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya gargadi mutane musamman ma’aikatan kiwon lafiya kan kiyaye sharudan guje wa kamuwa da cutar zazzabin Lassa.

Adewole ya ce yin wannan gargadin ya zama dole musamman yadda bana cutar ta yi wa ma’aikatan kiwon lafiya kwantan bauna inda suka yi ta fama dashi

Ya ce bisa ga rahotanin da suka samu daga hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa NCDC ya nuna cewa cutar ta yi ajalin ma’aikatan asibiti 10 a jihohin Ebonyi, Kogi da Ondo sannan mutane da dama na kwance a asibitoci sanadiyyar kamuwa da cutar.

Domin hana maimaicin irin haka Adewole ya fadi hanyoyi 5 da mutane da ma’aikatan kiwon lafiya za su iya bi don guje wa kamuwa da cutar kamar haka;

1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.

2. Ya ce duk ma’aikacin kiwon lafiyan da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbatar yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbatar ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiyar.

3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zaran alluran da suka yi afani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

4. A tabbatar an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci daga fitsari da kuma kashin beraye.

5. Ya ce ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da shi ya taba wanda ba shi da shi.

Share.

game da Author