Dalilin da ya sa muka saka dokar hana bin wasu hanyoyi a Barno – Jami’an tsaro

0

Kwamishinan aiyukkan cikin gida da al’adun gargajiya na jihar Barno Bukar Bulama ya yi shelar cewa gwamnati ta kafa dokar hana bin tituna uku da ababen hawa a jihar daga ranar 30 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Faburairu.

Ya ce titunan da aka hana bi sun hada da Konduga – Bama – Banki, Bama – Gwoza da Maiduguri – Damboa – Gwoza.

Bulama ya fadi cewa babban dalilin da ya sa gwamnati ta hana bin wadannan hanyoyi shine bisa ga shawara da rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ ta ba ta don samar da tsaro a wadannan ranaku da ta ayyana.

” Mun yi haka ne domin mu samar wa jami’an tsaro sauki na aikin da suke yi a yankin don kawar da sauran burbudin Boko Haram.”

Daga karshe Bulama ya yi kira ga mutane da su ba jami’an tsaro hadin kai.

Share.

game da Author